Makurdi: Ba za mu ji dadi ba idan Buhari bai ziyarci Binuwai ba – Inji Tor Tiv

Makurdi: Ba za mu ji dadi ba idan Buhari bai ziyarci Binuwai ba – Inji Tor Tiv

- Sakin Tor Tiv ya ce majalisarsa ba za ta ji dadi ba idan Buhari bai ziyarci Binuwai ba

- Sarkin ya bayyana hakan a wata ganawa da manema labarai a fadarsa na wucin gadi a garin Gboko

- Ayatse ya ce ziyarar shugaban kasa yana da muhimmanci sosai domin akwai bambanci tsakanin zuwansa da aika wakilci

Sarkin al’ummar Tiv a duk fadin duniya baki daya, Tor Tiv, Farfesa James Ayatse, a ranar Talata, 9 ga watan Janairu ya bayyana cewa majalisarsa na gargajiya ba za ta ji dadi ba idan shugaba Muhammadu Buhari ya kasa ziyarci jihar Binuwai domin ya gani da idonsa abubuwan da ya faru a jihar.

Ayatse wanda ya bayyana hakan a wata ganawa da manema labarai a fadarsa na wucin gadi a garin Gboko, ya ce ko da yake ya gamsu da kokarin shugaban wanda kuma ya gabatar da wakilci a jihar a makon da ya gabata, amma ya kamata ya zo da kansa.

"Wannan jiha ta yi ruwa da tsaki a zaben sa a matsayin shugaban kasa, saboda haka a wannan lokacin da aka yi muna kisan gilla, aka kuma kone gidajenmu, muma cikin baƙin ciki, muna buƙatar ziyarsa. Shugaban kasa bai zo ba tukun na, amma muna fata zai zo”.

Ya ce, "Ziyararsa yana da muhimmanci sosai domin akwai bambanci tsakanin zuwanka da aika wakilci. Idan bai zo ba, ba za mu ji dadi ba", in ji shi.

KU KARANTA: Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari, da gwamna Ortom sun gana a cikin Aso Rock

Idan dai baku manta ba Legit.ng ta ruwaito cewa shugaba Muhammadu Buhari ya gana da gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom a fadar shugaban kasa a yau Talata don tattauna a kan kashe-kashen kwanan nan da ya auku a jihar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng