Abuja: Fadar shugaban kasa ta zargi Mark, Tambuwal da sauransu da laifin cin hanci
- Fadar shugaban kasa ta zargi Mark, Tambuwal da sauransu da laifin cin hanci a majalisar na bakwai
- Gwamnati ta ce kasawar majalisar ta bakwai ya haifar da zargin cin hanci da rashawa a karkashin gwamnatin Jonathan
- Fadar shugaban kasa ta ce rashin kula na majalisar tarayya a wancan lokacin ya haifar da zargin almubazzaranci da kudaden tsaro
Fadar shugaban kasar Najeriya a ranar Talata, 9 ga watan Janairu, ta zargi shugabannin majalisar tarayya ta bakwai, bisa zargin rashin kula da ma'aikatu, sashe da hukumomi (MDAs).
Rahotanni daga jaridar Sun ta bayyana cewa, fadar shugaban kasa ta kuma ci gaba da cewa kasawar majalisar ta bakwai ya haifar da zargin cin hanci da rashawa da kuma sata dukiyoyin al’ummar kasar, wanda ta zama ruwan dare a karkashin gwamnatin da ta shuda na Goodluck Jonathan.
Legit.ng ya tattaro cewa sanata David Mark ya kasance shugaba na majalisar ta shida da bakwai, yayin da gwamnan Sakkwato, Aminu Tambuwal, ya kasance a matsayin shugaban majalisar wakilai a majalisar na bakwai.
Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa a kan al'amura na majalisar tarayya, Ita Enang, ya bayyana hakan yayin da yake jawabi da manema labarai na majalisar a ranar Talata, 9 ga watan Janairu.
KU KARANTA: kungiya ta tsayar da Buhari da Masari a zaben 2019
Ya ce rashin kula na majalisar tarayya a wancan lokacin ya haifar da zargin almubazzaranci da kudaden tsaro wanda aka yi wa tsohon mashawarcin tsaro na kasa (NSA), Kanal Sambo Dasuki (mai ritaya) da sauran wadanda suka yi aiki a karkashin gwamnatin Jonathan da aka ambaci sunan su.
Enang wanda kuma memba ne na majalisar na bakwai, inda ya kasance shugaban kwamitin dokoki da kasuwanci.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng