Da walakin goro a miya: Matasan dake kai hare hare a jihar Benuwe da sunan Fulani sun shiga hannu
Karshen tika! Tika! Tik! Inji bahaushe, a ranar Lahadi 7 ga watan Janairu ne dubun wasu matasan kabilar Tibi ta cika, inda Allah ya tona asirin su yayin da suke dauke da muggan makamai.
Rundunar Yansandan jihar Benuwe ce ta samu nasarar cafke wadannan miyagun matasa a ranar Lahadin data gabata, inda ta bayyana su a matsayin masu fakewa da sunan Fulani suna kai munanan hare hare.
KU KARANTA: Jagoran Kwankwasiyya ya samu kyakkyawar tarba a jihar Katsina
Majiyar Legit.ng ta ruwaito da matasan suka ji matsi, sun tabbatar ma da zargin da ake yi musu, inda suka shaida cewar suna kai hare hare kauyukan Tibi dake jihar Benuwe, don jama’a su dinga ganin kamar Fulani makiyaya ne suke kai harin.
Idan za’a tuna an samu yawaitan hare hare a kauyukan jihohin Kaduna, Benuwe, Nasarawa, Taraba da kuma Adamawa, inda ake danganta hare haren da tsatstsamar dangantaka dake tsakanin Makiyaya da manoma.
A kokarin sa na shawo kan matsalar, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci babban sifetan Yansandan daya tattara ya koma jihar Benuwe don tabbatar an magance hare haren, haka zalika ya gayyacin gwamnan jihar, Samuel Ortom zuwa fadar Villa don tattauna batun.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng