Wata sabuwar amarya ta sanyawa angonta gubar abinci har lahira a jihar Kano
Hukumar 'yan sandan jihar Kano ta cafke wata matashiyar amarya, Sadiya Umar, bisa aikata laifin sanyawa angonta, Umar Sani gubar abinci har lahira bayan makonni biyu da daura musu aure a jihar Kano.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, wannan ibtila'a da abin al'ajabi ya afku ne a unguwar Yakasai dake cikin tantagwaryar birnin jihar Kano a ranar Alhamis din makon da ya gabata.
Rahotanni sun bayyana cewa, marigayi Umar ya rigamu gidan gaskiya ne bisa zargin amaryarsa da ake na sanya masa gubar bera cikin abincinsa a ranar Alhamis din makon da ya gabata, inda ya cika bayan kwana guda a asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano.
KARANTA KUMA: Bincike: Kasashe goma mafi kankantar farashin man fetur a duniya
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, DSP Magaji Musa Majiya, shine ya bayyana hakan a wata ganawar wayar tarho da manema labarai a Daily Trust, inda yace an cafke Malama Sadiya ne a ranar Litinin din da ta gabata bayan kwanaki biyu da ta ari kafar kare.
Majiya yake cewa, 'yan uwa uku na marigayin ne suka shigar da kara a ofishinsu na kofar Wambai da yayi sanadiyar cafke ta bayan da jami'ai suka gudanar da sintiri har na kwanaki biyu.
LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng