Dalilin da yasa na je kasashe 97 a matsayin shugaban kasa - Obasanjo
Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a ranar Talata ya ce ya ziyarci kasashe 97 a lokacin mulkinsa a matsayin shugaban kasa tsakanin 1999 da 2007.
Yace ziyarar nashi kasashe ba don komai bane illa gyaro martabar kasar bayan shekaru da dama da tayi a mulkin sojoji.
Mista Obasanjo yayi matukar Allah wadai da kashe kashen makudan kudade kan tafiye tafiyen kasashen waje.
Amman tsohon shugaban ya bayyana a jawabinsa a ranar Litinin a jami’ar Oxford cewa tafiye tafiyensa sun janyo muhimman amfani ga tattalin arzikin kasar.
“An zabeni a mukamin shugaban kasar Najeriya a Febreru 1999 kuma aka rantsar dani a Mayu 1999."
Yace “Ko ina mutane sun kasance da matalaucin ra’ayi kanmu. An mana wulakanci an kuma daukemu a matsayin nauyi a jerin kasashe.
KU KARANTA KUMA: Abinda na fadawa gwamna Ortom dangane da hare-haren Fulani a jihar Benuwe yayin ganawar mu - Buhari
“Al’amarin ya bukaci inyi aiki don janye wannan fahimtan. A matsayin kasa dake karkashin canjin siyasa, na gabatar da kaina kwarai da gaske ga aikina.
“A shekaru takwas na shugabancina, na kai kuka ga sauran shuwagabannin duniya na kuma cigaba da yin hakan sama da shugabancina. Wannan ya kasance jigilar diflomasiyya a shugabanci.
“Nayi tafiya sosai, don neman fahimtar duniya da kuma al’adarmu cikin cikin sabuwar umurnin duniya- ba ga Najeriya ba kadai, amman ga Afirka gaba daya. A lokacin da na gama mulkina, nayi tafiye-tafiye zuwa ga kasashe 97," a cewar Obasanjo.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng