Mafi yawan ‘yan siyasar Najeriya barayi ne – Inji Obasanjo

Mafi yawan ‘yan siyasar Najeriya barayi ne – Inji Obasanjo

- Obasanjo ya ce mafi yawan ‘yan siyasar Najeriya ‘yan fashi da baro ne

- Obasanjo ya bayyana cewa marigayi Umaru Musa Yar'Adua ya rushe tsarin da ya gabatar don hana cin hanci da rashawa

- Tsohon shugaban ya ce babban kuskure na farko da Yar'Adua ya tafka shine cire tsohon shugaban hukumar EFCC, Nuhu Ribadu

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana a ranar Litinin, 8 ga watan Janairu cewa marigayi tsohon shugaban kasa, Umaru Musa Yar'Adua ya rushe tsarin da ya gabatar don dubawa da kuma hana cin hanci da rashawa a kasar.

Ya bayyana cewa cire tsohon shugaban hukumar EFCC, Nuhu Ribadu, shine babban kuskure na farko da Yar'Adua ya tafka.

Ya ce Yar'Adua ya yarda da bukatar tsohon gwamnan jihar Delta, James Ibori, a kan maye gurbin Ribadu, wanda ya yi zargin cewa an yi masa guba, amma ya tsallake rijiya da baya.

Mafi yawan ‘yan siyasar Najeriya barayi ne – Inji Obasanjo
Tsohon shugaban kasar Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo

Obasanjo ya bayyana wadannan a cikin wata hira da jaridar Thisday.

KU KARANTA: Abuja: Fadar shugaban kasa ta zargi Mark, Tambuwal da sauransu da laifin cin hanci

Legit.ng ta tattaro cewa, tsohon shugaban ya nuna damuwa matuka game da yawan kuɗin da ake bukata a harkokin siyasa a yau.

Ya ce, "Mutanen da suka sace dukiyoyin al’ummar kasar masu ubangida sune suka mallaki harkokin siyasa a Najeriya, irin da muke da shi yanzu a majalisar tarayya”.

“Saboda haka, ya kamata matasan Najeriya su shiga harkokin siyasa don maye gurbin wadannan shugabannin yanzu da kuma samar da shugabanci na gari da suka dace”.

"Na tsawon shekaru takwas da ni ke mulki, na yi ƙoƙarin tattauna da sauran shugabannin duniya ta hanyar diflomasiyya wajen ƙoƙarin neman a saukaka muna bashin da ake bin mu wanda kuma muka yi nasara", in ji shi.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng