Kungiyar Barcelona ta gabatar da Coutinho ga magoya bayanta

Kungiyar Barcelona ta gabatar da Coutinho ga magoya bayanta

Barcelona ta gabatar da Philippe Coutinho a gaban magoya bayanta a Camp Nou a yau ranar Litinin, bayan ya saka hannu kan yarjejeniya da kungiyar.

Dan wasan Brazil, mai shekara 25 ya koma Spaniya da murza-leda kan kudi da ake tunanin sun kai fam miliyan 160, bayan da Liverpool ta amince da cinikin a ranar Asabar.

Legit.ng dai ta samu cewa dan wasan ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekara biyar da rabi a gaban shugaban Barcelona Josep Maria Bartomeu.

Kungiyar Barcelona ta gabatar da Coutinho ga magoya bayanta
Kungiyar Barcelona ta gabatar da Coutinho ga magoya bayanta

Kuma duk kungiyar da take son daukarsa sai ta biya fam miliyan 355 idan kwantiraginsa bai kare a Barca ba.

Coutinho ya dauki hoto a Camp Nou da wasu 'yan wasa da jami'ai, bayan da Barcelona ta doke Levante 3-0 a gasar La Liga a ranar Lahadi.

Barcelona ta gabatar da Coutinho ga magoya bayanta da misalin karfe 11:30 agogon GMT a jiya Litinin a Camp Nou.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng