Allah-daya-gari-banban: An hallata sayar da tabar wiwi a Amurka
A yanzu an halatta sayar da tabar wiwi domin nishadi a kasuwanni jihar California dake a tarayyar kasar Amurka dake zaman wata doka mai cike da cece-kuce.
Sai dai kawo yanzu kamar yadda majiyar mu ta shaida mana, shaguna kadan ne a wasu biranen jihar su ke da izinin sayar da ita.
KU KARANTA: Yunkurin sayar da jarirai ya janyo wa wata uwa matsala
Legit.ng dai ta samu cewa a kwanan baya ma hukumar hana fasa-kwauri ta Najeriya ta kama tabar wiwi mai dumbin yawa a cikin motar wata jami'a a kan iyakar kasar da Jamhuriyyar Benin.
Hukumar Kwastam ta shaida wa manema labari a Lagos cewa ta kama tabar wiwi mai dumbin yawa a cikin motar jam'iar Abeokuta da ke kudancin kasar.
A ranar Talata ne wani babban jami'in hukumar na shiyyar kudu maso yammacin Najeriyar, ya ce sun kama motar ne dauke da tabar wiwi a kan iyakar kasar da Jamhuriyyar Benin.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng