Siyasa: Buhari zai ziyarci Abia a yau Talata
- Shugaba Buhari da mataimakinsa za su ziyarci Abia a yau Talata
- Shugabannin biyu za su halarci gangamin taron jam’iyyar APC wanda za a gudanar a jihar
- Sakataren hulda da jama’a na APC ya ce an kammala shirye-shiryen karɓar bakunci shugaban kasa
An kaddamar da tsaro a Umuahia babban birnin jihar Abia, a shirye-shiryen ziyarar shugaban kasa, Muhammadu Buhari da mataimakinsa, Yemi Osibanjo, zuwa jihar a yau Talata, 9 ga watan Janairu.
Za su kasance a jihar ne don halartar gangamin taron jam’iyya mai mulki ta APC.
Za a gudanar da taron a filin wasa na Umuahia wato ‘Umuahia Towship Stadium’ wanda ke a kan hanyar ‘School Road’ a babban birnin jihar.
Shugaban jam’iyyar APC, Cif John Odigie-Oyegun da shugaban gwamnonin jam’iyyar, gwamna Rochas Okorocha da kuma sauran manyan jiga-jigan jam’iyyar daga yankin kudu maso gabas da kuma kasar baki daya za su halarci wannan babban taron.
KU KARANTA: Kudin kasar wajen Najeriya ya haura Dala Biliyan 40 - CBN
Dukkanin manyan wuraren shiga da fitowar zuwa Umuahia an saka jami’an tsaro masu dauke da makamai a shirye shiryen ziyarar shugaban kasar.
Sakataren hulda da jama’a na APC, Mista Benedict Godson, wanda ya bayyana wa majiyar Legit.ng a ranar Litinin, ya ce an kammala shirye-shirye don karɓar bakunci shugaban kasa.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng