Farashin man fetur din Najeriya shine mafi sauki a duniya
- Najeriya tana cikin jerin kasashe 10 dake sayar da man fetur akan farashi mai sauki a duniya
- Jaridar Bloomberg ta ce farashin man fetur din Najeriya shine mafi sauki a duniya
Sabuwar rahoto da ya fito daga jaridar Bloomberg ya nuna cewa farashin da ake sayar da litan man fetur a Najeriya shine mafi sauki a duniya akan naira N145 a kowani lita daya wanda yayi daidai da dala $0.40.
Wannan ya sa Najeriya ta shiga cikin jerin kasashe 10 da ake sayar da litar man fetur da sauki a duniya sabanin yadda aka sayar da shi a kasuwar duniya a farashin $1.45 na lita daya wanda yayi daidai da N625 a kudin Najeriya.
A cikin matsalolin da Najeriya ke fuskanta shine, duk da fitar da miliyoyin gangan danyen mai da Najeriya keyi a kowani rana, Najeriya tana shigo da man fetur daga kasar waje saboda lalacewa matatun man kasar.
KU KARANTA : Miyetti Allah ta yi Allah wadai da kisan da aka yi a jihar Benuwe
Kuma mafi akasarin kasashen nahiyan Afrika basu da matatun mai.
Farashin mai abu ne mai matukar tasiri a rayuwan yan Najeriya, ganin yadda gwamnotocin kasar basa yiwa yan kasar aiki da zai kawo musu cigaba, karanci farashin man fetur ne kadai yan Najeriya suke samu da sauki daga wajen gwamnatin su.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng