Kasar Iran ta haramta koyar da turanci a makarantun firamare

Kasar Iran ta haramta koyar da turanci a makarantun firamare

- Kasar Iran ta haramta koyar da yaren Turanci a makarantun firamare

- Ta ce ta yi hakan ne domin kakkabe tasirin al'adun Amurka a kan 'yan kasar

- Daga yanzu koyar da yaren Turanci a makarantun firamaren gwamnati da masu zaman kansu haramun ne a kasar Iran

Kasar Iran ta cire yaren Turanci daga manhajar ilimin firamaren kasar domin dakile tasirin al'adun Amurka a kan 'yan kasar ta, kamar yadda shugaban hukumar ilimin kasar, Mehdi Navid-Adham, ya bayyana.

Kasar Iran ta haramta koyar da turanci a makarantun firamare
Ayatollah Khomeini

"Daga yanzu koyar da yaren Turanci a makarantun firamaren gwamnati da masu zaman kansu ya sabawa dokar kasar Iran. Akidu na shiga mutum ne tun yana karamin yaro. Muna son yaranmu su taso da akidu da al'adu na kasar Iran ba na Amurka ba," a cewad Mehdi.

Ana koyar da yaren Turanci ne a makarantun firamare ga yara 'yan shekaru 12 zuwa 14, wasu makarantun kan koyar da yaren ga yara 'yan kasa da shekaru 12. Makarantu masu zaman kansu a kasar na amfani da yaren Turanci wajen koyarwa.

DUBA WANNAN: Isra'ila ta bawa 'yan Afrika wa'adin barin kasar ko ta garkame su a gidajen yari

Shugaban koli na kasar Iran, Ayatollah Ali Khomenei, ya ce haramta koyar da Turancin a makarantun firamare ba yana nufin kiyayya ga yaren kasashen ketare ba ne, saidai ya ce ba zasu bawa al'adun kasashen ketare fifiko sama da nasu na gida ba.

Ana ganin kasar ta Iran ta dauki wannan mataki ne saboda goyon bayan zanga-zangar nuna kyama ga gwamnatin kasar da shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi.

Hukumomin kasar sun ce a kalla mutane 22 sun mutu yayin da aka kama wasu fiye da 1,000 tun bayan barkewar zanga-zangar a biranen kasar sama da 80.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng