Matan Saudiyya zasu halarci kallon kwallon kafa a ranar Juma’a karo na farko
Za’a yarje ma mata a kasar Saudiyya da su halarci wasannin kwallon kafa a ranar Juma’a karo na farko a masarautan, a cewar hukumomi a ranar Litinin.
Mata masoyan kwallon kafa zasu shiga babban filin wasa na masarautan don halartan wasannin kwallon kafa uku wanda zai hada da wasannin gida a matsayin gasar Saudi Professional League competition, a cewar hukumar sadarwa na gwamnatin a wata sanarwa.
Za ayi wasannin uku ne a ranar Juma’a, Asabar da ranar 18 ga watan Janairu, a Karin jawabin.
A watan Oktoba, hukumar wasanni na Saudi, tace daga farkon 2018 za’a shirya filin wasanni uku, har da filin wasa na maza kadai ga iyalai, hade da ware sarari don zama da sararin shiga.
Sun hada da filin wasan King Fahd International Stadium a birnin Riyadh, Birnin wasa daga yammacin birnin Jeddah, da filin wasan Yarima Mohammed bin Fahd a Damman dake gabashin Saudiyya.
A watan Satumba, sarkin saudiyya bin Salman ya bayar da umurni na yardar wa mata tukin mota, wannan ya keta al’ada da ta dade a masarautan.
KU KARANTA KUMA: Malamai sun rufe kofofin shiga makarantu a Kaduna, El-Rufai ya maida martani
Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman ne ya jagoranci dage haramcin kamar yanda yake kokarin bude kasar da canja martabar kasar ga duniya.
Mista Mohammed, mai shekaru 32 ya sha alwashin cewa masarautan zata koma “Matsakaicin Musulunci” kamar yanda yake aiki kan rage albarkacin cibiyoyin addini a kasar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng