Buhari ya yi burus da halin da muke ciki, hakurina ya fara karewa - Gwamnan jihar Benuwe

Buhari ya yi burus da halin da muke ciki, hakurina ya fara karewa - Gwamnan jihar Benuwe

- Gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom, ya ce shugaba Buhari ya share su duk da halin da suke ciki

- Ortom ya zargi wasu hadiman shugaba Buhari da kange shi daga ganin shugaban kasar

- Gwamnan ya ce hakurinsa ya fara karewa

Gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom, ya ce shugaba Buhari ya yi burus da halin da mutanen jihar Benuwe suke ciki.

Da yake zantawa da jaridar Vanguard, Ortom, ya ce duk kokarinsa na ganin shugaba Buhari domin fayyace masa su waye keda hannu a cikin rikicin dake faruwa a jihar Benuwe ya ci tura. Gwamnan ya zargi wasu hadiman shugaba Buhari da kange shi daga ganawa da shugaban kasar saboda wata manufa ta kashin kansu.

Buhari ya yi burus da halin da muke ciki, hakurina ya fara karewa - Gwamnan jihar Benuwe
Gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom.

"Maganar gaskiya gwamnatin tarayya ba ta yi wani kokari ba domin shawo kan matsalar da muke ciki duk da irin rahotanni na tsaro da muka aike ofishin mai bawa shugaban kasa shawara a kan tsaro da shugaban hukumar tsaro na farin kaya (DSS). Har da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, saida na sanar halin da muke ciki a jihar Benuwe a lokacin da yake rikon kwaryar mulki amma duk hakan bai saka an dauki matakan warware matsalar da tuntuni muka hango ba," Ortom ya bayyana.

DUBA WANNAN: Zargin Fulani makiyaya da kisan mutum 33 ya jawo barkewar zanga-zanga a Benuwe

Ortom ya kara da cewar "yanzu ga shi lamarin ya lalace har ta kai ga jama'a sun fara daukan doka a hannunsu. Ban so a kai ga hakan ba. Maganar gaskiya ni hakurina ya fara karewa."

Kazalika gwamna Ortom ya bayyana yadda kungiyoyin Fulani na Miyetti Allah da Kautal haure Fulbe suka yi watsi da dokar hana Fulani makiyaya kiwo da jihar ta kafa. Yana mai bayyana hakan a matsayin raini ga ikon da jihar keda shi na yin dokokin da zasu inganta zaman lafiya a jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng