Sabuwar rikici ta ɓarke a jihar Taraba, sama da mutum 20 sun halaka
Wani sabon rikici ya barke a karamar hukumar Lau dake jihar Taraba wanda yayi sanadiyyar mutuwar sama da mutane ashirin, kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito balahirar ta shafi wasu kauyuka da suka hada da Lau, da Katibu, kamar yadda wani mazaunin kauyen ya shaida mata.
KU KARANTA: Yan fursuna sun tarwatsa gidan Yari, sun fantsama cikin gari
“Muna zargin Fulani makiyaya ne suka kai wannan harin, inda suka yi harbe harbe tare da cinna ma gidajen mu wuta, a yanzu haka mun samu gawar mutane 25, haka zalika akwa wasu daban da suka tsere, amma maharan suka bi su a kan babura suka bindige su.” Inji shi.
Sai dai Kaakakin rundunar Yansandan jihar, David Simal yayi karin haske game da lamarin, inda yace tun a ranar Juma’a aka fara kai harin, har zuwa Lahadi, 7 ga watan Disamba.
“Jama’a da dama sun jikkata a sakamakon harin, amma bamu tabbatar da adadin mamatan ba.” Inji shi.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng