Zabe: APC ta ki amince da sakamakon zaben kananan hukumomin Delta
- PDP ta lashe 23 daga cikin 25 na kananan hukumomin jihar Delta a zaben da aka gudanar a ranar Asabar
- APC ta ce ba ta amince da sakamakon zaben ba saboda an tafka babban magudi
- Shugaban hukumar zabe a jihar ya ce an jinkirtar da zabe a kananan hukumomin biyu saboda rikicin da ya barke a yankunan
Babban jam'iyyar adawa ta PDP ta lashe 23 daga cikin 25 na kananan hukumomin jihar Delta a zaben da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata a fadin jihar.
Kamar yadda Legit.ng ke da labari , shugaban hukumar zabe mai zaman kanta a jihar Delta (DSIEC), Mike Ogbodu, ya sanar da sakamakon zaben a ranar Lahadi a Asaba, babban birnin jihar.
Ya ce an jinkirtar da zabe a kananan hukumomin Ethiope ta gabas da Ughelli ta arewa, saboda rahotanni game da tashin hankalin da ya haifar da konewar ofishin DSIEC a Ughelli.
Ya ce za a sake gudanar da zabe a wadannan kananan hukumomin biyu a Janairu 9, 2018.
KU KARANTA: Zaben 2019: Takarar shugabancin kasa ta Gwamna Dankwambo ta kara samun tagomashi
Ogbodu ya ce jam'iyyar ta PDP ta kuma lashe kujerun kansiloli 424 a fadin jihar, inda ya kara da cewa 'yan takara 59 na PDP sun dawo ba tare da wata amayya ba.
Ya kuma bayyana cewa ba a kada kuri'a na kansila ba a Ward 2 da Ward 4 a yankin karamar hukumar Oshimili ta arewa.
Ya ce ba a gudanar da zabe a wuraren biyu ba saboda hukuncin kotu, wanda ta hana gudanar da zaben.
A cewarsa, jam'iyyar APC ta lashe zaben kansila guda daya tak a Ward 2, a yankin karamar hukumar Aniocha ta arewa.
Duk da haka, jam’iyyar APC a jihar ta ki amince da sakamakon zaben, ta ce an tafka babban magudi.
Shugaban jam’iyyar APC a jihar, Mista Jones Erue, ya bayyana matsayin jam'iyyar a wata sanarwa da aka bayar ga manema labarai ranar Lahadi a Asaba.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng