Sharukh Khan ya gindaya sharudda 6 da duk saurayin da ke son ‘yar sa

Sharukh Khan ya gindaya sharudda 6 da duk saurayin da ke son ‘yar sa

Shahararren Jarumin nan na Bollywood, Shah Rukh Khan ya gindaya wasu dokoki ga duk saurayin da zai ce ya na son ‘yar sa Suhana mai shekaru 16 zuwa 17.

Jarumin wanda uba ne ga ‘yaya uku; Aryan Suhana da Abram, ya bayyana cewa yana matukar son ‘yayan nasa kuma yana sanya masu ido ya kula da su yadda ya kamata.

A wata Hira da ya yi, jarumin ya bayyana cewa duk saurarin da zai ce yana son ‘yar sa to sai ya:

1. Kasance ya na da aikin yi

2. Fahimci cewa shi Sharukh Khan baya son shi

3. Ya samo lauya mai tsaya masa

Sharukh Khan ya gindaya sharudda 6 da duk saurayin da ke son ‘yar sa
Sharukh Khan ya gindaya sharudda 6 da duk saurayin da ke son ‘yar sa

KU KARANTA: Dalilin da ya sa nayi wa Umma Shehu tambayar addini - Aminu Momo

4. Ya sani cewa Suhana Gimbiyar Shahrukhan ce, ba wata kyauta ba da ya ciwo

5. Ya sani cewa shi Sharukh Khan ba ya tsoron komawa gidan yari

6. Ya sani cewa duk abunda ya yi wa yarsa sai ya rama mata.

Jarumin dama dai ya dade yana sanya ido akan irin samarin da ke kusantar ‘yar ta sa, kuma da alama ya yi wannan magana ne domin ya razana su.

Jarumin wanda a kwanan nan ya samu lambar yabo a matsayin gwarzon uba na kasar Indiya ya bayyana cewa tun da ya taso kawo yanzu ya koyi darussa da dama musamman a gurin matan da ya ke harkokin fim da su, ya ce wannan darussa su suka sa ya damu akan ‘yarsa kuma ba zai bari wani namiji ya bata mata ba.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng