Har yanzu bamu sani ba ko Buhari zai kara tsayawa takara a 2019 - Oyegun

Har yanzu bamu sani ba ko Buhari zai kara tsayawa takara a 2019 - Oyegun

- Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Cif John Oyegun, ya ce basu sani ba ko Buhari zai tsaya takara

- Ya ce jam'iyyar ba ta karbi kowanne sako daga shugaban kasa a kan tsayawa takarar ba

- Ya bayyana cewar dole shugaban ya sanar da jam'iyyar APC kafin ya tsaya takarar

Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Cif John Odigie-Oyegun, ya sanar da cewar jam'iyyar ba ta da masaniyar ko shugaba Buhari zai kara tsayawa takara a zaben shekarar 2019.

Oyegun ya ce jam'iyyar APC ba ta karbi kowanne sako daga shugaba Buhari a kan batun tsayawa takara ba.

Har yanzu bamu sani ba ko Buhari zai kara tsayawa takara a 2019 - Oyegun
Shugaban Jamiyyar APC na kasa; Oyegun

Rahotanni sun bayyana cewar shugaba Buhari ya bayyana aniyar sa ta kara tsayawa takara a zaben shekarar 2019 kuma har ma ya nada Ministan harkokin sufuri, Rotimi Amaechi, a matsayin jagoran yakin neman zabensa.

DUBA WANNAN: Ba za'a yi magudi a zaben shekarar 2019 ba - INEC

Da yake tsokaci a kan wannan magana, Oyegun, ya shaidawa jaridar New Telegraph a karshen satin da ya wuce cewar shugaba Buhari bai sanar da jam'iyyar hakan ba; da baki ko a rubuce. Kazalika ya bayyana cewar wajibi ne shugaba Buhari ya sanar da jam'iyyar niyyar sa ta sake son tsayawa takara kafin ya bayyana hakan ga jama'a.

"A jaridu nima na karanta cewar shugaba Buhari zai kara tsayawa takara a zaben shekarar 2019 amma a jam'iyyance bamu da masaniyar hakan. Amma ko da gaske zai kara tsayawa ko sabanin haka, dole zai sanar da jam'iyya," inji Oyegun.

A dangane da alkawuran da jam'iyyar APC ta dauka yayin yakin neman zabe, Oyegun, ya ce jam'iyyar ta fita kunyar mutanen Najeriya musamman a bangaren farfado da tattalin arzikin Najeriya da kuma aiyukan raya kasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel