Dandalin Kannywood: Jaruma A'isha Tsamiya ta sanar da komawar ta makaranta

Dandalin Kannywood: Jaruma A'isha Tsamiya ta sanar da komawar ta makaranta

Fitacciyar jaruma A'isha Aliyu da ake yi wa lakani da Tsamiya ta bayyana cewa ta samu gurbin karo karatu a Budaddiyar Jami'ar Njeriya, wato National Open University of Nigeria (NOUN).

A wata hira da aka yi da ita a gidan talbijin na Arewa24, jarumar ta bayyana cewar za ta karanta kwas din 'Health Technology' ne.

A amsar wata tambaya da mai gabatar da shirin "Kundin Kanbywood", wato Aminu A. Shariff da aka fi sani da Momoh, ya yi mata, A'isha ta ce, "Yanzu na samu admission a Open University. Ina so in karanci Health Technology."

Dandalin Kannywood: Jaruma A'isha Tsamiya ta sanar da komawar ta makaranta
Dandalin Kannywood: Jaruma A'isha Tsamiya ta sanar da komawar ta makaranta

KU KARANTA: Tunina dakin miji na nike sha'awar yin fim - Hadizan Saima

To amma majiyar mu ta mujallar Fim ta gano cewa ba a yin wannan kwas din a jami'ar.

Daraktan Watsa Labarai na jami'ar, Malam Ibrahim Sheme, ya fada wa mujallar Fim cewa, "Health Technology bai cikin jerin kwasakwasan da wannan jami'ar ke gudanarwa. Amma kwas din da jami'ar ke yi wanda ya kusanci abin da A'isha Tsamiya ke so ta karanta shi ne 'Public Health'."

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng