Mabiya addinin Shi’a sun y kira ga Buhari da babban murya
Mabiya addinin Shi’a sun gudanar da gagarumin zanga zanga a garin Potiskum na jihar Yobe, inda suka yi kira ga gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya sako musu jagoransu, Ibrahim Zakzaky.
Yan Shi’an sun fara zanga zangar ne daga unguwar Kara, zuwa Asibitin Musa Lawan a ranar Lahadi 7 ga watan Janairu na shekarar 2018, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
KU KARANTA: Barka: Sojojin Najeriya aika wani gagararren mai laifi
Shugaban yan Shi’ar, Malam Ibrahim Lawan yace gwamnatin tarayya na cigaba da rike shugaban su, duk da cewa manyan Kotuna sun yanke hukuncin a sake shi, tun ba yau ba.
“Lafiyar shugaban mu Ibrahim Zakzaky na cigaba da tabarbarewa sakamakon cigaba da kama shi da gwmanati ke yi ba’a kan ka’ida ba, kuma gwamnati ta yi haka ne don ganin ta hallaka shi.
“Don haka muna kira a sako mana shugaban mu, don samun ingantaccen kulawa, bai kamata gwamnati ta cigaba da rike shi.” Inji shi.
Daga karshe Malam Lawan ya bayyana godiyarsa ga dukkanin kungiyoyin dake basu goyon baya a fafutukar da suke yi a Najeriya.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng