Dalilin da yasa muka kai harin mai kan uwa da wabi a jihar Benuwe- Inji Fulani Makiyaya
Shuwagabannin kungiyar Fulani makiyaya na jihar Benuwe sun bayyana dalilin da yasa yan Fulani suka kai wani mummunan hari a wani kauyen jihar Benuwe, inda suka kashe mutane 17 a sabuwar shekarar 2018.
Shugaban kungiyar Miyetti Allah reshen jihar, Garus Gololo ya bayyana ma jaridar BBC cewar matsalar ta samo asali ne a lokacin da wasu bata gari suka shiga satar shanun Fulani yayin da suke kan hanyarsu ta barin jihar zuwa makwabtan jihohi biyo bayan kaddamar da sabuwar dokar hana kiwo a jihar.
KU KARANTA: Sojojin Najeriya aika wani gagararren mai laifi
“A lokacin da muke tsallakawa jihar Nassarawa, wasu barayi sun sace mana shanu 1000, wannan ne dalilin da yasa muka yi ramuwar gayya.” Inji Gololo.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito harin ramuwar gayyar a Fulani suka kai ya shafi kauyukan Gaambe-Tiv, Ayilamo, Turn, Umenger, Tse-Akor da Tomaater dake kananan hukumomin Guma da Logo.
Tun a baya rahotanni sun tabbatar da zaman dar-dar a jihar tun bayan tabbatar da dokar hana kiwo a jihar sakamakon yawaitan fadace fadace tsakanin Fulani makiyaya da manoma, wanda Fulanin ke ganin ba’a yi musu adalci ba.
Sai dai, wannan harin ya harzuka matasan jihar, inda suka nuna bacin ransu ta hanyar kona tayoyi a kan titunan jihar da kuma tare da manyan hanyoyin jihar, tare da bukatar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shawo kan lamarin.
Dayake yin jawabi ga manema labaru, Kaakakin gwmanatin jihar, Terve Akase ya bayyana cewa tun da misalin karfe tara na asubahin ranar Litinin yan Fulanin suka kaddamar da hare haren har zuwa karfe 4 na asubah.
Shi ma a nasa bangaren, Kaakakin rundunar Yansandan jihar, Moses Yamu ya tabbatar da mutuwar mutane 17, sa’annan ya bayyana suna cigaba da binciken lamarin, tare da kama mutane 8.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng