2019: Tun yanzu ka fara shirin zaman gidan kaso – Inji PDP ga gwamna Bello
- PDP ta ce za a tura keyar gwamna Bello zuwa kurkuku bayan wa’adin mulkinsa
- Jam’iyyar ta bayyana cewa dole ne gwamnan ya yi bayani game da kudaden da ya karba a madadin al’ummar jihar
- PDP ta ce a nan gaba dokar kariya ba za ta kare shi ba don haka ya shirya
Babban jam'iyyar adawa ta PDP ta ce gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, zai fuskanci zaman kurkuku bayan ya kammala wa’adinsa a matsayin gwamnan jihar idan ya kasa bada bayani game da kudaden da ya karba a madadin al’ummar jihar.
Jami’in hulda da jama’a na jam’iyyar a jihar Kogi, Mista Bode Ogunmola, ya bayyana hakan a yayin ganawar da yi da jaridar Daily Post a ranar Lahadi, 7 ga watan Janairu.
Ogunmola wanda ke amsawa ga sanarwar da aka bawa gwamnan Bello cewa ya ciwo bashin N10 biliyan domin ya biya bashin albashin ma'aikatan jihar, ya ce ya damu matuka irin kalu balen da wannan matakin zai iya jawo wa gwamnati a nan gaba.
Ogunmola ya ce, "Idan wani ya ce ya ciwo bashin N10 billion, idan lokaci ya gabato zai zo ya nuna mana littafin. Idan kuma ya kasa bayar da bayani a kan kudaden da ya ciwo bashi a madadin al’ummar jihar, to, zai fuskanci sakamakon abin da ya yi".
KU KARANTA: Lokoja: Gwamnatin Kogi ta yi ritaya sakatare na dindindin 8, sa'a nan ta sallami ma'aikata 1,774
"Amma zan iya tabbatar cewa wani zai bakwanci gidan yari akan wannan saboda a nan gaba dokar kariya ba za ta kare shi ba kuma za'a tambayi shi yadda ya yi amfani da dukiyar jama’a da kuma laifin da ya aikata a baya", Inji shi.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng