An yi jana'izar Fulani 15 da aka kashe a Taraba
- An samu barkewar rikicin kabilanci a jihar Taraba ranar Juma'a
- Rikicin ya barke ne tsakanin kabilar Bachama da Fulani a karamar hukumar Lau
- Fulani 15 sun mutu sanadin rikicin
Wani rikici mai nasaba da kabilanci da ya barke a garuruwan Katibu, Donadda, da Babagasa a karamar hukumar Lau ta jihar Taraba tsakanin kabilar Bachama da Fulani ya yi sanadiyar salwantar rayukan Fulani 15.
Saidai Fulanin sun musanta afkuwar barkewar kowanne rikici tare da bayyana cewar 'yan kabilar Bachama ne suka kai masu hari haka siddan suka kashe masu mutane.
Rahotanni sun samu mabanbantan adadin Fulanin da aka kashe yayin harin. Yayin da wasu kafafen yada labaran suka ce mutum 7 ne suka mutu, wasu sun ce sun fi haka.
.Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN), ya bayyana cewar an kai harin a kauyukan Babagasa, Donadda, da katitbu dake iyaka da jihar Adamawa da misalin karfe 6:00 na safiyar ranar juma'a.
DUBA WANNAN: Hukumar soji ta tabbatar da kashe gagararren dan ta'adda mai garkuwa da mutane
Kakakin hukumar 'yan sanda a jihar Taraba, ASP David Misal, ya tabbatar da binne Fulani hudu da suka mutu sakamakon harin, adadin da mutanen kauyukan da abin ya shafa suka musanta. kazalika ya ce har ya zuwa yanzu hukumar 'yan sanda bata san su waye suka kai harin ba kuma basu kama kowa dangane da harin ba. Ya yi kira ga jama'ar kauyukan da su cigaba da rayuwar su yayin da hukuma ke cigaba da binciken al'amarin.
Rikicin na jihar Taraba ya shiga sahun rigingimu masa alaka da kabilanci dake faruwa a Jihar Benuwe tsakanin Manoma da Fulani makiyaya da kuma hare-haren ta'addanci a jihar Ribas.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng