Ruwa ya ci wasu 'yan mata hudu a jihar Jigawa

Ruwa ya ci wasu 'yan mata hudu a jihar Jigawa

- Ruwa ya ci wasu 'yan mata hudu a jihar Jigawa

- 'Yan matan na kokarin tsallaka kogin ne a kauyen Sakwaya dake karamar hukumar Dutse

- Hukumar 'yan sanda ta tabbatar da mutuwar 'yan matan

A yau ne kakakin hukumar 'yan sanda a jihar Jigawa, DSP Abdu Jinjiri, ya sanar da cewar wasu 'yan mata hudu sun mutu a kauyen Sakwaya yayin da suke kokarin tsallaka wani kogi ya zuwa wani kauye a jiya, Asabar.

Ruwa ya ci wasu 'yan mata hudu a jihar Jigawa
Ruwa ya ci wasu 'yan mata hudu a jihar Jigawa

'Yan matan sun rasa ransu ne yayin da suke kokarin tsallaka kogin domin samo itacen girki a wani kauye da ake kira Farantawa.

'Yan matan da suka mutu, kamar yadda kakakin ya sanar, su ne; Sumayya Gadi, mai shekaru 7; Zuwaira Abdulmumin, mai shekaru 12; Gaji Sa'idu, mai shekaru 12; da Ummi Sa'idu, mai shekaru 11.

DUBA WANNAN: Gawurtaccen mai garkuwa da mutane ya fada komar 'yan sanda a jihar Jigawa

Yaran sun gamu da ajalinsu ne bayan da iyayensu suka aike su domin samo itacen girki a kauyen Marantawa dake tsallaken kogi, karkashin karamar hukumar Albasu dake jihar Kano.

Jinjiri ya ce an tabbatar da mutuwar yaran a asibiti mafi kusa, kuma tuni aka binne su kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. Ya kara da cewar wasu 'yan uwa ga yaran ne suka sanar da hukumar 'yan sanda afkuwar lamarin a jiya, Asabar, da misalin karfe 1:30 na rana.

Ya shawarci iyayen da suke saka ido a kan dukkan zirga-zirgar 'ya'yansu tare da kira ga jama'ar gari da su ke bayar da taimakon gaggawa ga mutanen da suka fada wani hatsari ko yanayin da kan iya jawo asarar rai ko ko lahani ga lafiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng