Jaridu na Najeriya: Abubuwa 10 da ya kamata ku sani a wannan safiyar ranar Lahadi
Taƙaitaccen labaran Najeriya daga jaridu daban-daban na safiyar yau Lahadi, 7 ga watan Janairu inda wasu 'yan Najeriya ke bayyana ra'ayoyinsu game da al'amuran kasar.
Wadannan ne taƙaitaccen labaran yau daga jaridu na Najeriya:
1. Hukumar 'yan sanda a ranar Asabar da ta gabata ta tabbatar da kashe wasu karin mutane 10 wanda ake zargin Fulani makiyaya suka aikata a yankin karamar hukumar Logo da ke jihar Binuwai.
2. Shugaban kungiyar Miyetti Allah reshen jihar Binuwai, Garus Gololo ya ce hare-haren da Fulani makiyaya suka kai a kan al’ummar jihar Binuwai wata matakin daukar fansa ne ga zargin satar shanu
3. Olubunmi Okogie, Arbishop na Katolika na Legas, ya shawarci shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya koma gida ya huta a 2019.
4. Kamfanin albarkatun man fetur na Najeriya, NNPC, ta sake jaddada cewa babu wani shiri na kara farashin man fetur a kasar.
KU KARANTA: 'Yan ta'addan Boko Haram 1,050 sun miƙa wuya ga dakarun soji a gabar tafkin Chadi da Monguno
5. Jigo a jam'iyya mai mulki ta APC, Bola Tinubu, ya karyata zargin da ake yada cewa yana goyon bayan burin tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar na neman shugabancin Najeriya.
6. Shugaban jam’iyyar APC, Cif John Odigie-Oyegun, ya bayyana cewa, jam'iyyar ba ta da hannu wajen tattara sunayen wadanda ake bukata a ba mukamai wanda suka kunshi mattatu.
7. Rundunar sojin Najeriya a ranar Asabar da ta gabata ta tabbatar da cewa kimani ‘yan ta’adda 1, 050 sun mika wuya ga dakarun da ke yankin Chad da Monguno.
8. Mai wallafa mujallar na Ovation, Dele Momodu, ya rubuta budediyar wasika zuwa ga shugaba Muhammadu Buhari bayan jita-jitar cewa zai nemi sake tsaya takara a shekara ta 2019.
9. Tsohon babban wakilin Najeriya a kasar Kanada kuma sanata a Jamhuriyyar ta biyu, Farfesa Iyorwuese Hagher, ya caccaki shugaba Muhammadu Buhari kan yadda ya yi shurun game da ci gaba da kisan kiyashi da ake yi wa al’ummar Najeriya wadanda ya yi alkawari zai kare su.
10. Cif Edwin Clark, ya bayyana cewa jawabin da shugaba Muhammadu Buhari ya yi na sabuwar shekara ba na 'yan Najeriya bane.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng