Bayan shekaru 4,700 da mutuwa, Masana sun gano sahun kafar Fira'auna
- Masana a kasar Masana sun gano sahun kafar Fira'auna
- Har yanzu ba a taba samun kwarangwal mai girman ta Fir'auna
- An tabbatar da sahun Fir'auna ne saboda girman sahun
Fir'auna ya yi sarauta a kasar Masar shekaru 4,700 da suka wuce kuma tun bayan mutuwar sa har yanzu ba a binne gawar sa ba, tana nan an adana ta domin tarihi.
Wasu masana dake binciken albarkatun karkashin kasa ne suka gano sahun kafar na Fir'auna a cikin wani kogo dake yamma da garin Beit Khalifa dake kasar Masar. An tabbatar da sahun kafar na Fir'auna ne saboda girman sahun, domin babu wani mahaluki a yanzu da yake da irin wannan girman kafa, kuma bincike ya nuna cewa wurin ya taba zama fadar mulkin Fir'auna.
DUBA WANNAN: Hotuna masu kayatarwa daga wani bikin nishadi da aka gudanar a Maiduguri
Tarihi ya nuna cewar Fir'auna mutum ne mai girman gaske, domin babu wani mutum a zamanin da muke ciki da ya kai kwatankwacin girmansa. Hakazalika bincike ya tabbatar da cewar har yanzu ba'a taba samun kwarangwal da ya kai girman na Fir'auna ba.
Shugaban masu binciken, Francesco M. Galassi, na jami'ar Zurich ta kasar Switzerland, ya bayyanaana cewar zasu kara zurfafa bincike domin tabbatar da cewar Fir'auna ya taba zama a dai-dai inda suka samu sahun kafar shi.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng