Dandalin Kannywood: Dalilin da yasa nayi ma Umma Shehu Tambaya akan addini - Aminu Momo
Shahararren jarumin fina-finan Kannywood Aminu Sheriff, wato Momoh ya wanke kansa daga zargin da ake yi masa cewa ya tozarta wata 'yar fim a shirin nasa lokacin da ya yi mata tambayar da ake gani ba ta shafi harkar fim ba.
A cewarsa, ya yi wa Umma Shehu tambaya kan addinin Musulinci ne bayan ta bayyana masa cewa ba ta damu da kallon fina-finai ba saboda tana zuwa makaranta.
KU KARANTA: An yankewa matar nan da ta kusa saida jariran ta hukunci a Arewa
Legit.ng dai haka zalika ta samu cewa Aminu Sheriff, wanda ya soma fim sama da shekara 20 da suka wuce, ya fara ne da rubuta fina-finai kafin ya soma fitowa a matsayin jarumi.
Ya rubuta fina-finai irinsu Mugun Nufi, A yi dai Mu Gani da Dr Gulam.
Fim din da ya soma fitowa a ciki shi ne 'Al-Mustapha' wanda suka fito tare da fitaccen jarumi Alhaji Kabiru Maikaba.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng