Dandalin Kannywood: Tun a dakin miji na na nike sha'awar yin fim - Hadizan Saima
Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Kannywood Hadiza Muhammad, wacce aka fi sani da Hadizan Saima ta bayyana cewa cewa ta soma sha'awar fina-finai ne tun lokacin da take da aure.
A cewarta, "Karance-karancen littafai da kallon fina-finan tarihi ne suka sa na soma sha'awar shiga fim.
"Na kalli fim din 'Ki Yarda Da Ni' a lokacin ina gidan mijina, kuma da aurena ya zo karshe sai na ji sha'awar shiga fim.
KU KARANTA: Yadda aljannu suka tarwatsa taron biki a Katsina
Legit.ng ta samu cewa jarumar ta bayyana cewa ta soma fim ne sama da shekara 16 da suka wuce kuma ta fito a fim fiye da 300.
"Wani darakta ne marigayi Tijjani Ibrahim ya tambaye ni irin rawar da na fi so na taka a fim, ni kuma na ce masa na fi son fitowa a matsayin uwa.
"Shi ya sa tun daga wancan lokaci nake fitowa a matsayin uwa, tun ma ina da kuriciya ake yi min kwalliya irin ta uwa domin na taka irin wannan rawar."
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng