Hotunan manyan mata yan kwalisa 5 da suka caba kayattacen ado a 2017
A cigaba da kawo maku fitattun al'amurran da suka faru a shekarar 2017 da ta wuce, yau ma gamu dauke da wani rahoton sabon salo na manyan mata iyaye kuma 'yan kwalisa da suka caba kayattacen ado a 2017:
1. Haj. Aisha Buhari
Wannan dai ita ce uwar gidan shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari. Tabbas kuma a duk inda taje ta kan bar kowa yana sakin baki saboda iya kwalliyar ta da kuma tsabar kyaun ta.
Duk da dai ba ta yadda hakan ya sa ta rabu da ainihin shigar ta ta Hausawa da Fulani ba da kuma addinin musulunci, ta kan sanya kayan ado masu tsadar gaske irin su zinare da tagulla.
2. Haj. Faiza Baba Ahmed
Wannan ma dai ta ciri tuta a shekarar da ta gabata ta 2017 don kuwa a yayin bikin diyar ta ta caba adon da ya sa duniyar masu kwalliya da ado girgiza kuma ba a bar maganar ta ba har shekarar ta kare.
KU KARANTA: Yadda aljannu suka firgita gayu a wurin biki a Katsina
Hajiya Faiza Baba Ahmad dai mata ce ga tsohon mataimakin Gwamnan Jigawa.
3. Haj. Jamila Musa Jalo
Ita ma dai wannan ta caba adon da ya girgiza duniyar ado da kwalliya a shekarar ta 2017.
Duk da ta dan manyanta tare kuma da haihuwa, Hajiya Jamila Musa Jalo da ta fito daga jihar Adamawa hakan bai sa ta rage kyau ko karsashi ba.
4. Uwar gida Pariya
Masu sharhi kan harkokin ado da kwalliya dai su kan yi mata lakani da kankana - wadda take kara zaki sadda take tsufa.
Kusan dukkan kayayyaki da kuma ado na yi wa wannan matar kyau matuka saboda kwarewar ta a fannin kwalliya da kwalisa.
5. Haj. Fatima Allamin Kam-Salem
Wannan ma dai dole a sakata a jerin sunayen manyan mata iyaye yan kwalisa da suka shana a 2017 in dai har rubutun zai kammalu.
Dama dai mata daga kabilar Shuwa Arab in dai batun kyau ne ba'a magana don kuwa sunyi fice duk duniya.
Asali: Legit.ng