Likitocin Najeriya 50,000 ke aiki a kasashen ketare

Likitocin Najeriya 50,000 ke aiki a kasashen ketare

A halin yanzu, babu kasa da likitoci 5,000 na Najeriya dake aiki a kasar Birtaniya kamar yadda binciken jaridar Leadership na karshen mako ya bayyanar.

Binciken diddigi da hukumar kula da lafiya ta Najeriya ta gudanar a kwana-kwanan nan ya bayyana cewa, a cikin adadin likitoci 'yan asalin tsatson nahiyyar Afirka dake aiki a kasar Birtaniya, kasar Najeriya ce ke da kaso mafi girma.

Akwai kuma kasashen Ghana da Afirka ta Kudu dake bi mata baya, inda adadin likitocin su dake aiki a nahiyyar turai suke a matakan 2,342 da kuma 1,641. A cikin binciken kuma, akwai likitoci 40 'yan asalin kasar Liberia dake aiki a kasar Birtaniya, wanda ta zamto mafi kasa wajen adadin likitocin da suka yi mata kaura.

Binciken karshen mako na jaridar Leadership ya bankado kididdigar kamar haka: Mauritania; 1234, Masar; 1026, Kenya; 705, Sierra Leone; 511, Uganda; 480, Zambia; 469, Sudan; 469, Somalia; 250, Gambia; 207, Malawi; 205, Libya; 150, Congo; 147, Eritrea; 147, Nijar; 124, Tanzania; 144, Afirka ta Tsakiya; 90, Algeria; 79, Morocco; 51, Cote d'Ivoire; 48, Rwanda; 49 sai kuma kasar Bostwana; 46.

Ministan Lafiya na Najeriya; Farfesa Isaac Adewole
Ministan Lafiya na Najeriya; Farfesa Isaac Adewole

Daga kididdigar kuma, Najeriya tana da likitoci 80,000, sai dai sama da 50,000 na aikinsu ne a kasashen ketare, inda kaso 92 cikin 100 na adadin wadanda suka yi saura a kasar suna yunkurin ficewa da kasar a halin yanzu.

KARANTA KUMA: Shugaba da mambobi 7000 na jam'iyyar APC sun yi sauyin sheka zuwa PDP a jihar Bayelsa

Kamar yadda wani shugaban sadarwa, Adedeji Adeleye, ya bayyana cewa muddin ba a tashi an farga akan wannan lamari ba, to kuwa wataran za a wayi gari babu likita ko guda a asbitocin gwamnati dake fadin kasar nan.

Adedeji yayi kira ga gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, akan ta tashi tsaye wurjajan domin kawo karshen wannan kalubale da kuma barazana dake fuskantar kasa baki daya.

LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng