Gwamnan Yobe ya baiwa sojoji kyautar motoci 20 masu tsadar gaske
Gwamnan jihar Yobe dake a yankin arewa maso gabas mai suna Gwamnan Ibrahim Gaidam ya baiwa jami'an rundunar sojin Najeriya kyautar manyan motocin shiga daji na Hilux guda 20 domin taimaka masu wajen yakin da suke yi da ta'addanci.
Gwamnan dai haka zalika ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta siya motocin ne akan kudi Naira miliyan 305 domin taimakawa kokarin gwamnatin tarayya wajen ganin an murkushe ayyukan ta'addanci.
Legit.ng ta samu cewa shugaban rundunar sojin ta kasa Laftanal Janar Yusuf Buratai da ya karbi motocin a maimakon rundunar ya godewa gwamnan bisa kokarin nasa sannan kuma ya sha alwashin cigaba da aiki ba dare ba rana har sai sun maido da zaman lafiya a yankin da ma kasa baki daya.
A wani labarin kuma, likitocin rundunar sojojin saman Najeriya sun taimakawa dubban 'yan gudun hijira ajihohin Borno, Adamawa da wasu wurare a arewa masa gabashin Najeriya kamar yadda babban hafsan sojojin saman Najeriya y shaidawa manema labarai.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng