Dandalin Kannywood: Na tafka kura-kurai da dama a rayuwata - Adam Zango
Fitaccen jarumin fina-finan Hausa, Adam A. Zango ya ce ya yi kura-kurai da yawa a rayuwarsa.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook da Instagram, Zango ya ce amma lokaci bai kure masa na gyara su ba.
Legit.ng ta samu cewa jarumin dai ya wallafa cewa: "Na yi kura-kurai da yawa a sanadiyyar daukaka...sai dai lokaci bai kure min ba!! Gyara ya zama dole...Allah ya ba mu sa'a".
Sai dai dan wasan kwaikwayon na Kannywood bai yi cikakken bayani kan abin da yake nufi ba, sai dai a wata hira da BBC a kwanakin baya, ya ce ya yi nadamar fitowa a fina-finai da dama.
Jarumin ya ce wani abu da yake ci masa tuwo a kwarya shi ne yadda wasu 'yan boko suke masa kallon jahili duk kuwa da cewa "na yi karatun bokon sannan kuma ina da ilimin addini."
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng