Yawaitar satar mutane: Gwamna El-Rufai ya soki gwamnatin Buhari a kaikace
Gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-Rufai da ma wasu sun ce dole ne gwamnatin tarayya ta yaki masu haddasa muggan ayyukan kamar yadda take yakar Boko Haram ta kuma kawar da wasu abubuwan dake haifar da wadannan munanan dabi'u.
Gwamna Nasiru El-Rufai ya ce gwamnatinsa ta yi iyakar tata kokarin saboda batun satar mutane ba a Kaduna kawai ya tsaya ba. Jihar ta dauki duk matakan taimaka wa jami'an tsaro su shawo kan lamarin a jihar, inji gwamnan.
Legit.ng ta samu cewa a cewar gwamna El-Rufai, a gwamnatance an gaya wa gwamnatin tarayya ta baza jami'an tsaro cikin duk dazuzzukan da wadannan bata-garin ke fakewa ciki, a yake su yadda ake yaki da Boko Haram. Gwamnan ya ce dole ne a yi amfani da sojojin kasa da na sama da kuma 'yan sanda a fatattake su.
Jama'ar yankunan da lamarin yafi kamari dai a baya sun sha sukar gwamnatin tarayya karkashin shugabancin shugaba Muhammadu Buhari da yi wa batun rikon sakainar kashi.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng