Legas: Wani dan Chadi ya kashe abokinsa saboda bai ba shi aron tabarau ba
- Wani matashi ya halaka abokinsa saboda bai ba shi aron tabarau ba
- Sosan ya soki abokinsa da wuka a kirji yayin da suke fada a ranar sabuwar shekara
- Marigayin mai suna Sanni dan yankin arewacin Najeriya ne, Sosan kuma da asalin kasar Chadi ne
Wasu Abokai biyu, Yusuf Sanni da Ahmed Sosan, sun rabu da mummunar labari bayan wani fada da ta barke a tsakanin su a kan titin Alhaji Alla da ke Morcas, Agege, jihar Legas.
Majiyar Legit.ng ta tabbatar da cewar, Sosan wanda dan asalin kasar Chadi ne ya soki Sanni a kirji yayin da suke fada a ranar sabuwar shekara.
Wannan fada dai tsakanin abokanai biyu ya faru ne sakamakon marigayin ya ki ya bawa abokinsa aron tabarau.
Jaridar PUNCH Metro ta tattaro cewa Sosan ya ziyarci Sanni, wanda yake da zama a kan titin Alhaji Alla, ya sadu da shi a gaban gidansa, yayin da yake hira da wasu abokansa.
KU KARANTA: Sojojin Operation lafiya Dole sun kashe dinbin ‘Yan Boko Haram a Yankin tafkin Chadi
Rahoton ta ce Sosan ya nemi ya ara tabarau wanda marigayin yake amfani da shi, amma ya ki yarda da bukatar.
Daga bisani, Sosan ya yi ƙoƙarin kwace gilashin da karfi, nan ne al’amarin ta rikice ta zama wani mummunan fada, amma Sanni ya rinjaye shi inda ya nakada masa dukar a kawo wuka.
Wani mazauni, wanda ya bayyana kansa a matsayin Sikiru, ya ce bayan da aka raba su, Sosan ya koma gida cikin fushi, 'yan mintoci kaɗan sai ya dawo tare da wuka wansda ya ɓoye a cikin tufafinsa.
Yayin da suka sake komawa fada, sai ya fitar da wukar kuma ya soki Sanni a kirji. A nan jini ya fara zuba daga hanci da bakin Sanni, nan da nan mutane suka ruga shi zuwa asibiti. Amma Allah ya yi masa cikawa kafin a iso da shi asibitin.
Sikiru ya ce, "Matashin biyu sun kasance abokai. Yusuf (Sanni) ya fito daga arewa ne, yayin da Ahmed (Sosan) ya fito daga kasar Chadi kuma yana tare da iyayensa”.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng