An yi yunkurin tsige ni daga kujera na – Inji shugaban APC

An yi yunkurin tsige ni daga kujera na – Inji shugaban APC

- Oyegun ya ce an nemi a cire shi a matsayin shugaban jam’iyyar APC

- Shugaban APC ya ce ya bijirewa shugabancin jam’iyyar ne saboda kokarin raba shi da mukaminsa

- Kungiyar Bini National Congress (BNC) ta ba Cif John Odigie-Oyegun lambar yabo a garin Benin-City

Shugaban jam'iyyar APC, Cif John Odigie-Oyegun, ya ce yawan kokarin neman cire shi daga ofis ya haifar da nuna rashin amincewarsa ga shugabancin da aka kafa a jam’iyyar.

Cif Oyegun, wanda ya bayyana hakan a lokacin da ya samu lambar yabo daga kungiyar Bini National Congress (BNC) a babban birnin jihar Edo, Benin-City a ranar Alhamis, 4 ga watan Janairu, ya bayyana cewa irin wannan yunkurin wani abin takaici ne wajen cimma burin jam'iyyar.

Kamar yadda Legit.ng ke da labari, shugaban a cikin wata sanarwa da aka bayar a ranar Laraba a Abuja, ya yi bayanin yadda ya tsira daga kokarin tsige shi daga ofishin a matsayin shugaban jam'iyya mai mulki.

An yi yunkurin tsige ni daga kujera na – Inji shugaban APC
Shugaban jam'iyyar APC, Cif John Odigie-Oyegun

KU KARANTA: Majalissar dattawa ta soki Abba Kyari

Ya ce: "Lokacin wannan lambar yabo yana da muhimmanci sosai ganin cewa kwanan nan na tsira daga wani yunkurin juyin mulki. Kungiya ta Bini, ‘yan uwana su ce ‘oga’ muna so mu girmama ka, abin alfahari ne gare ni kuma ina tsammanin na cancanci girmamawar. Na gode da wannan lambar yabo.”

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng