Yanzu-Yanzu: An kai hari a kan gwamnan jihar Edo
- Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a kan gwamnan jihar Edo
- Ana zargin babban daraktan kamfanin BUA’s yana da hannu a harin
- BUA da kamfanin simintin Dangote suna rikici a kan mallakar wani ma'adinai a Okpella da ke jihar Edo
Kakakin gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya saki wata sanarwa cewa an kai hari ga gwamnan a jihar.
Robin Crusoe ya kuma bayyana cewa an ba da umarnin kama babban daraktan BUA’s Obu Cement Company, Yusuf Binji wanda ake zargi yana da halaka game da harin.
Kamar yadda Legit.ng ke da labari, BUA da kamfanin simintin Dangote sun kasance cikin rikici a kan mallakar wani ma'adinai a Okpella da ke jihar Edo.
Gwamnatin jihar ta tsayar da duk wani aiki a wurin kuma a ranar Laraba, 3 ga watan Janairu ya jagoranci jami'an tsaro inda aka kama wasu ma'aikatan BUA guda biyu wadanda ake zargi da ci gaba da aiki.
KU KARANTA: Ya kamata shugaba Buhari ya sake shiri akan harkokin tsaro na kasa - Dickson
A ranar Alhamis, Mista Crusoe ya nakalto 'yan sanda wadanda suka bayyana cewa Mista Binji yana da hannu a harin da aka kai wa gwamnan.
Zamu kawo muku karin bayani...
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng