Hotuna: An gudanar da wani biki na nishadi a Maiduguri
- An gudanar da wani taro domin nishadi a Maiduguri
- Taron manuniya ce a kan irin cigaban da aka samu ta fannin tsaro a garin
- An gudanar da taron ne ranar biyu ga watan Janairu
Wasu matasa, Maza da Mata, sun gudanar da wani taro a garin Maiduguri domin kawai su yi nishadi. Matasan sun gudanar da taron ne ranar Talata, 2 ga watan Janairu, 2018.
Wannan taro na matasa tamkar ma'auni ne na dawowar zaman lafiya a garin na Maiduguri da ya dade yana fama da hare-haren ta'addanci daga mayakan kungiyar Boko Haram.
DUBA WANNAN: Dubi dumbin dukiyar da aka kwato daga hannun shugaban kungiyar matsafa a Legas
Da yake yada hotunan a dandalin sada zumunta, mai taimakawa shugaban kasa a bangaren yada labarai ta kafafen sada zumunta, Bashir Ahmad, ya bayyana cewar shekaru uku da suka wuce babu wanda zai iya fitowa koda kofar gidansa ne da sunan yin nishadi balle har a yi taron gangami domin kawai a yi nishadi, a ci, a sha, sannan kuma a dauki hotuna.
Bashir ya mika godiya ga shugaba Buhari bisa namijin kokarin da ya yi wajen dawowa da mutanen Maiduguri 'yancinsu na yin rayuwa ba tare da tsoron wani ko wata kungiya za ta kai masu hari ba. Kazalika ya yi jinjina ga shugaban rundunar sojojin kasa, Tukur Buratai, da kuma dakarun soji da suka sadaukar da rayuwar su domin tabbatar da zaman lafiya a jihar Borno da yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng