Yan sanda sun kama wata mata da gawar jarirai 2 cikin firjin
Yan sanda a kasar Jamus sun sanar da samun nasarar cafke wata mata mai shekaru 46 tare da jarirai biyu matattu a cikin firjin din ta a wani gari da ake kira Benndorf.
Yan sandan sun bayyana cewa sun samu bayanan sirri ne game da wannan aika-aikar da matar tayi ta bakin tsohon saurayin ta inda ya kwarmatawa 'yan sandan cewar jariran sun dade a ajiye.
Legit.ng haka nan kuma ta samu cewa 'yan sandan sun tabbatar wa da manema labarai cewa za su kaddamar da bincike domin gano musabbabin ajiye jariran da kuma yadda akayi ta same su.
A wani labarin kuma, wani mutum mai suna Innocent Pitman da ake zargi da lakadawa uban sa duka sakamakon sabanin da suka samu ya samu beli a kotu mai matsayi na daya a unguwar Karu, garin Abuja babban birnin tarayya.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng