Dandalin Kannywood: Tsohuwa ta taba tsine mun saboda fim - Sadiq Ahmad
Babban jarumin nan mai suna Sadiq Ahmad ba boyayye bane ba sam a harkar fim domin kuwa yana cikin tsirarun masu harkar da suka fito daga garin Jos da kuma tauraruwar su ke haskawa a masana'antar Kannywood din.
Sai dai jarumin ya bayyana wani abun al'ajabi da ya taba cin karo da shi a dalilin sana'ar sa inda ya ce wata tsohuwa ta taba tsine masa saboda rawar da yake takawa a fina-finan sa.
KU KARANTA: Wanda ya lakadawa uban sa duka ya samu belin Naira dubu 100
Legit.ng ta samu cewa jarumin ya bayar da wannan labarin ne a cikin zantawar da yayi da wata mujallar dake kawo rahotannin lamurran Kannywood din.
Jarumin ya bayyana cewa akwai wani lokacin da suke daukar shirin su na fim inda wata tsohuwa ta tsine masa albarka.
Ya kara da cewa a lokacin kuma da ya tambayeta ko menene dalilin hakan sai 'yar da ke tare da tsohuwar ta ce masa saboda ya cutar da jaruma Hadiza Gabon a cikin fim din 'Daga Ni Sai Ke'.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng