Gwamnatin jihar Yobe ta bawa sojin Najeriya tallafin motoci 20

Gwamnatin jihar Yobe ta bawa sojin Najeriya tallafin motoci 20

- Gwamnatin jihar Yobe ta bawa sojin Najeriya kyautar motoci 20

- Ta bawa sojin kyautar filaye domin gina makaranta da asibiti

- Gwamnan jihar ya ce kyautar ta nuna jin dadin aikin da sojin ke yi a jihar ne

Gwamnan jihar, Ibrahim Geidam, ya mika makullan motocin ga shugaban rundunar sojin kasa na kasa, Tukur Buratai, a gidan gwamnatin jihar a yau. Buratai yana jihar Yobe ne a cigaba da ziyarar da yake yi ta sansanin sojoji dake jihohin arewa maso yammacin Najeriya.

Gwamnatin jihar Yobe ta bawa sojin Najeriya tallafin motoci 20
Gwamnatin jihar Yobe ta bawa sojin Najeriya tallafin motoci 20

Gwamna Geidam ya ce kyautar ta nuna jin dadi ce ga aiyukan samar da zaman lafiya da sojojin ke yi a jihar da kuma kara masu karfin gwuiwa domin fatattakar ragowar 'yan ta'addar kungiyar Boko Haram a jihar. Ya zuwa yanzu gwamnatin jihar Yobe ta bayar da kyautar motoci ga hukumar soji da adadinsu ya kai 300.

DUBA WANNAN: An cafke kasurgumin mai garkuwa da mutane a jihar Jigawa

Da yake magana bayan karbar kyautar motocin, Buratai, ya jinjinawa gwamnan jihar bisa kokarinsa na tallafawa harkar tsaro a jihar da ma yankin arewa maso gabas baki daya.

Buratai ya kara da cewa, bayan kyautar motoci, gwamnatin jihar ta bayar da kyautar filaye kyauta ga hukumar sojin domin gina Makaranta a Buni Yadi da kuma Asibiti a Damaturu, babban birnin jihar. Tuni har an fara ginin asibitin kuma Buratai ya ziyarci wurin aikin domin ganin matakin da aiki ya ke.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng