Daliban kasar Sin da dama suna karatun digiri a harshen Hausa
- Harshen Hausa ta samu karbuwa a wajen daliban kasar Sin
- Daliban kasar Sin da dama sun wakilci Najeriya a lokacin bikin nuna al'adun kasashe da aka gudanar a jami'ar Peking dake Beijing
- Wani dalibi ya ce yana karatun digiri a harshen Hausa ne saboda mafi akasarin yan kasar sa basu san Najeriya ba
Alaka na diflomasiyya tsakanin Najeriya da kasar Sin ta fara ne tun shekaru 46 da suka gabata, amma duk da haka yan kasashen biyu ba su san komai game da al’adun juna ba.
A cikin wannan lokaci wasu daliban kasar Sin dake jam’iar Beijing na Peking suka fara karatun digiri a harshen Hausa.
A lokacin da aka gudanar da bikin al’adu na kasashen Duniya a jami’ar Peking a watan Oktoba na shekarar 2017, dalibi daya daga Najeriya tare daliban kasar Sin da dama suka wakilci Najeriya a wurin bikin.
Abun farinciki ne ganin yadda daliban kasar Sin suka yi shiga irin ta Hausawa a wurin bikin.
KU KARANTA : Gobara ta babbaka yara hudu a jihar Zamfara
Wani dalibi mai suna, Meng Xiang, wanda ya sanya babbar riga da hula baka, ya fadawa manema labaru cewa, yana karatun digiri a harshen hausa ne saboda mafi akasarin yan kasar Sin ba su san Najeriya ba.
Saboda haka yana son yayi amfani da wannan dama ya karfafa alaka tsakanin yan Najeriya da kasar Sin.
Alaka tsakanin Najeriya da kasar yana kara yin karfi, saboda shugabannin Najeriya suna kai wa kasar ziyara.
A shekaraer da ta gabata ne manyan ma’aikatan gwamnati suka ziyarci kasar Sin. A cikin su harda sarki Kano, Mai Alfarma sarki Muhammadu Sanusi II.
Wannan abu ya nuna muhimmacin koyan harusan Najeriya ga matasan kasar Sin.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng