Majalissar dattawa ta soki Abba Kyari
- Majalissar ta soki Abba Kyari akan kalaman da yayi game da wahalar man fetur da ake fuskanta a kasar
- Abba Kyari ya zargi majlissar dattawa da kin amincewa da bashin da gwamnati take so ta ciwo
Majalissar dattawa ta soki shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari, akan kalaman da yayi game da wahalar man fetur da ake fuskanta a kasar.
Mai magana da yawun bakin majalissar dattawa, Sabi Abdullahi, ya karyata kalaman da Abba Kyari yayi na cewa, gwamnati tarayya ta kasa biyan dilolin mai bashin da suke bin ta saboda majalissr ta ki amincewa da bashi da take so ta ciwo.
Majalissar Dattawa ta shawarci Abba Kayri ya daina kago karya dan ba wasu laifi.
KU KARANTA : Gobara ta babbaka yara hudu a jihar Zamfara
Sabi Abdullahi, ya ce Majalissar dattawa ta na son yan Najeriya su sani cewa babu lokacin da haka ya taba faruwa.
Majalisar ta ce, ta son wannan gwamnatin ta janye tallafin man fetur a kasar, saboda haka wani bashi gwamnatin take magana akai.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng