Mataimakin shugaban kasa na ci gaba da holewarsa a kasashen Larabawa na Gabas

Mataimakin shugaban kasa na ci gaba da holewarsa a kasashen Larabawa na Gabas

A halin yanzu, mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, yana ci gaba da holewarsa tare da shakatawa a kasashen larabawa na Gabas inda yake gudanar da hutunsa a shekara.

Legit.ng ta samu wannan rahoton ne da sanadin jaridar Premium Times, inda mabubbugar rahoton tazo da sanadin kakakin mataimakin shugaban kasar, Laolu Akande, inda ya bayyana a shafinsa na sada zumuntar twitter cewa, Mista Osinbajo ya bar Najeriya ne tare da uwargidansa da kuma 'ya'yan su.

Mista Akande ya bayyana cewa, mataimakin shugaban kasa Osinbajo, uwargidansa da 'ya'yansu suna ci gaba da shakatawa a kasar waje inda yake gudanar da hutunsa na shekara. Ana sa ran mataimakin shugaban kasar zai dawo Najeriya a karshen wannan mako daga kasashen larabawan Gabas.

Osinbajo da uwargidansa
Osinbajo da uwargidansa

A cikin gwamnatin shugaba Buhari, wannan shine karo na farko da mataimakin shugaban kasar ya samu damar shakatawa kamar yadda tsarin kasa ya tanadar masa na daukar hutu a duk shekara.

KARANTA KUMA: Yadda motsa jiki ke taimakawa wajen hana ta'ammali da sigari

A baya mataimakin shugaban kasar yayi fadi-tashi wajen dawainiya da Najeriya a yayin da yake mukaddashin shugaban kasa a lokutan da shugaba Buhari ya shafe yana jinya a birnin Landan na kasar Birtaniya.

A cewar Mista Akande, ya zamto abin raha a fadar shugaban kasa a duk lokutan da mataimakin shugaban kasar zai jagoranci wani taro musamman zaman majalisa, mutane su kan ce "lallai kam yau zamu zaunu".

LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng