Ministan tsaron na Nijar ya ce an murkushe Boko Haram a kewayen Tafkin Chadi
- Ministar Tsaro na Nijar yace dakarun hadin sun murkushe mayakan kungiyar Boko Haram
- Kalla Mukhtari ya ce har yanzu akwai dakarun sojojin Amurka da Faransa a Nijar
- Mukhtari ya ce kasar Nijar da Italiya sun fara karfafa huldar diflomasiya a tsakaninsu tsakanin su
Ministan tsaro na jamhuriyyar Nijar, Kalla Mukhtari, yace dakarun hadin gwiwa na kasashen yankin tafkin Chadi sun samu nasarar murkushe mayakan kungiyar Boko Haram a kewayen tafkin da sassan garin Diffa.
Kalla Mukhtari, ya bayyana haka ne birnin Niamey a taron manema labaru da ya kira gabanin shiga shekara 2018.
Minista yace har yanzu akwai yan fashi da makami da suke labewa a yankin Diffa domin yiwa mutane kwace.
Ya ce za'a kawo karshen sa a wannan sabuwar shekarar kamar yadda mayakan Sahel suka fara daidaita al'amura a kan iyakar kasar sa da Mali.
KU KARANTA : Isra'ila ta bai wa 'yan Afirka wa'adin kwana 90 su bar kasar ko a daure su
Da aka tambaye shi akan batun girke dakarun sojojin kasashen waje a cikin kasar Nijar, Ministan ya ce har yanzu dakarun Amurka da Faransa kawai suke da sansanoni a kasar.
Da aka kara tambayar sa akan yunkurin kafa sansanin yaki da ta'addanci da dakile hanyar da bakin haure ke bi zuwa Turai da kasar Italiya ta ke shirin yi a Nijar, Ministan ya ce maganar ba ta taso ba.
Ya ce yanzu ne ma kasashen biyu ke kokarin karfafa huldar diflomasiya tsakaninsu
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng