Isra'ila ta bawa 'yan Afrika masu ci-rani wa'adin barin kasar ko ta maka su a kurkuku
- Kasar Isra'ila ta bawa 'yan nahiyar Afrika wa'adin barin kasar
- Ta ce zata maka duk wadanda suka yi kunnen kashi a kurkuku
- Majalisar Dinkin Duniya ta ce kudirin na kasar Isra'ila ya sabawa dokar kasa da kasa a kan 'yanacin 'yan ci-rani
Kasar Isra'ila ta bawa 'yan nahiyar Afrika dake zaman ci-rani wa'adin barin kasar ko kuma ta maka su a gidajen yari.
Gwamnatin kasar Isra'ila ce ta bayyana hakan ne dubban 'yan ci-rani daga Afrika dake kasar, tare da yin barazanar dauri a kurkuku ga duk wanda ya ki barin kasar bayan karewar wa'adin a watan Maris.
Kasar ta ce za ta bawa kafatanin 'yan ci-ranin adadin dalar Amurka $3,500 ( miliyan N1.2) domin su bar kasar cikin kwanaki 90. Kazalika za'a bawa 'yan ci-ranin zabin komawa kasar su ta haihuwa ko kuma wata kasar da suke da shaidar zamanta.
Matukar kuma suka ki amincewa da hakan, kasar ta Isra'ila ta ce za ta fara kama su tana makawa a gidajen yari dake kasar.
Wani jami'i a hukumar kidaya da kula da shige da fice a kasar Isra'ila ya shaidawa BBC cewar a halin yanzu akwai 'yan ci-rani kimanin mutum 38,000 da suka shigo kasar ta barauniyar hanya kuma suke tsugune a sansanin baki daban-daban dake kasar..
DUBA WANNAN: Najeriya za ta sayi jiragen yaki na zamani a kan $593m daga kasar Amurka
"Da zarar watan Maris ya kare, duk wadanda suka amince su bar kasar Isra'ila zasu karbi guzurin tafiya. wadanda kuma suka yi taurin kan bin doka zamu dauki mataki mai tsanani a kansu", a cewar jami'in.
'Yan kasar Sudan da Eritrea ne suka fi yawa daga cikin 'yan ci-rani dake zaune a kasar ta Isra'ila. 'Yan kasashen na tserewa zuwa kasashen ketare saboda rigingimu dake addabar kasashensu.
Majalisar dinkin duniya ta ce wannan kudiri na kasar Isra'ila ya sabawa dokar kasa da kasa a kan a kan 'yan masu ci-rani.
Saidai Firaministan kasar Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya ce barin 'yan Afrika suke shuga kasar sasakai kan iya zama barazana ga kabilar Yahudu, wadanda sune keda mallakin kasar, tare da bayyana cewar tuni su sallami wasu 'yan ci-rani kimanin su 20,000 kuma ba zasu huta ba har sai sun fitar da ragowar 'yan Afrikan daga kasar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng