Wutar lantarki ta Najeriya ta samu tangarda
- An samu tangarda a wutar lantarki ta Najeriya
- An fara fuskantar matsalar wuta tun a daren jiya Talata
- Gobarar wuta a bututun makamashin gas ta janyo matsalar wuta a Najeriya
An samu yankewar wutar lantarki a daren ranar Talatar da ta gabata, wanda hakan ya janyo daukewar wuta dindim a fadin kasar nan baki daya.
Rahotanni sun bayyana cewa, wannan tangarda da aka samu ta zo ne da sanadin tsautsayi na gobara da ya afku a bututun makamashin gas na kamfanin Escravos dake jihar Edo.
Wannan lamari ne ya sanya aka datse shigar makamashin gas cikin bututun dake kaiwa zuwa injinan samar da wutar lantarki.
KARANTA KUMA: Kiwon Lafiya: Cututtuka takwas da karas yake kawarwa a jikin Dan Adam
Ma'aikatar wuta, kwadago da kuma gidaje ta tabbatar da faruwar hakan a wata sanarwa da misalin karfe 12:44 na daren ranar Laraba ta yau.
LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng