An haifi jarirai 20,210 a ranar 1 ga watan Janairu a Najeriya - UNICEF
- Najeriya ce kasa na uku a duniya da aka haifi jarirai masu yawa a ranar farkon shekara 2018
- Kungiyar UNICEF ta ce duk da yawan jararan da aka haifa a ranar farkon 2018 akwai jararai da yawa da suka mutu a ranar
- Kasar India ce na daya a cikin kasahen da aka fi haifi jarirai a ranar farko na sabuwar shekara
Hukumar kula da kananan yara dake karkashin Majalissar dinkin Duniya, UNICEF ta ce an haifi akalla jarirai 20,210 a rana 1 ga watan Janairu, na shekara 2018 a Najeriya.
Wannan adadin ya sa Najeriya ta zama kasa ta uku da aka fi samun yawar haihuwar jarirai a ranar farkon na sabuwar shekara
Kungiyar UNICEF ta ce an haifi jarirai akalla 360,000 a ranar farkon sabuwar shekara ta 2018 a duniya.
Hukumar ta ce rabin adadin jariran da aka haifa a ranar farkon sabuwar shekara daga kasashe Tara kacal aka haife su.
KU KARANTA : Makiyan Iran ne suka haddasa zanga-zanga- Khamenei
Ga jerin sunyaen kasashen da aka fi haifn jarirai da adadin su
1. India 69,070
2.China 44,780
3. Nageria 20,210
4.Pakistan 14,910
5. Indosia 13,370
6.Amurka 11,280
7.Congo 9,400
8.Ethipia 9,020
9.Bangladesh 8,370
Wani babban dan kungiyar UNICFE, Mr Stephen Peterson, ya bayyana cewa duk da yawan jariran da aka haifa a ranar farkon sabuwar shekara akwai jariran da yawa da suka mutu a ranar bayan an haife su.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng