Isra'ila ta bai wa 'yan Afirka wa'adin kwana 90 su bar kasar ko a daure su
- Yan Afrika suna fuskantar barazana daga gwamnatin Isra'ila
- Gwamnatin Isra'ila ta ba yan Afrika wa’adin kwana 90, su fice daga kasar ko su
- Dokar barin Isara'ila a cikin kwana 90 bai shafi shafi kananan yara da tsofaffi ba
Gwamnatin kasa Israila ta ba dubban bakin haure ‘yan Afrika wa’adin kwana 90, su fice daga kasar ko su fuskanci dauri a gidan kaso.
Sama da mutane 38,000 sun fadi jarabawar neman mafaka da kasar Isara’ila ta sa suka rubuta, mafi akasarin su ‘yan kasar Eritriya da Sudan ne.
Yanzu sai dai su koma kasashen su ko su ta fi kasar Yuganda ko Rwanda, kuma ba wa ko wannan su taimakon dala $3,500 dan kama hanya.
Sai dai wannan umarni bai shafi kananan yara, tsofaffi da wadanda suka kubuta da hanun masu fataucin dan Adam
KU KARANTA : Duk da harin da Fulani suka kai kauyukan jihar mu, ba za mu soke dokar hana kiwo ba – Gwamna Ortom
Hukumar kula da ‘yan gudun hijira na majalisar dinkin duniya MDD da kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun ce korar bakin haure ya sabda dokar kasa da kasa.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng