Kannywod ba za ta ci gaba ba sai an daina fina-finai maras Al-kibla - Aminu Sherrif Momoh
- Aminu Sherrif Momoh ya ce ya soma yin fim ne dan watsa harshe da al’adun Bahuashe
- Masana’atar fina-finan Hausa ba za ta cigaba ba sai an daina fina-finan da basu da al-kibla inji Momoh
Fitaccen dan wasan kwaikwayo na fina-finan Kannywood, Aminu Sherrif Momoh, yace masana’atar fina-finan Hausa ba za ta cigaba ba sai an daina fina-finan da basu da al-kibla.
Aminu Sherrif ya bayyana haka ne a wata hira da yayi da BBC Hausa a jihar Kano.
Fitaccen jarumin yace babban kalubalaen da suke fuskanta itace manufa daya da zai kai masana’antar gaba da kuma bunkasa harshen Hausa.
KU KARANTA : An bukaci shugaba Buhari ya sauka daga mukamin sa na ministan mai
“Amma idan aka cigaba da yin fina-finan Hausa marasa al-kibla babu inda za a kai,” inji Momoh.
Momoh yace manufar sa na shiga masana’antar fim din Hausa, shine bunkasa harshe da al’adun Hausa a kasashen duniya.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng