Fitattun 'yan Nigeria da suka mutu a 2017
- Legit.ng ta kawo muku jerin sunayen fitattun yan Najeriya da suka mutu a shekara 2017
- A cikin su akwai sarkuna, yan kasuwa da fitattun yan siyasar Najeriya
Ahmadu Chanchangi
Shaharrren dan kasuwa kuma shugaban kamfanin jiragen sama na Chanchangi Airlines, Alhaji Ahmadu Chanchangi, ya rasu a watan Afrilu.
Maragayi, Alhaji Ahmadu Chanchangi, ya rasu ya bar mata biyu, ‘ya’ya 33 a cikin su har da dan majalisar waikilai daga jihar Kaduna.
Danbaba Suntai
Danbaba Suntai, tsohon gwamnan jihar Taraba ne wanda ya rasu watan Yuni bayan ya shafe shekaru hudu yana jinya bayan yayi hatsari a cikin jirgin saman da yake tukawa da kan sa. Ya rasu yana da shekaru 56.
Yusuf Mataima Sule
A watan Yuli Allah yayiwa, Alhaji Yusuf Maitama Sule, Dan masanin Kano rasuwa a wani asibiti a kasar Masar. Dan Masani ya rasu yana da shekaru 88.
KU KARANTA : Zanga-zangar Kasar Iran : Abun da muka sani
Marigayi, Maitama Sule, Shahararren dan siyasa ne a Najeriya wanda ya taba rike mukamin minista a jamhuriyya na farko da kuma jakadan Majalissar Dinkin Duniya UN.
Dakta Alex Ifeanyichukwu Ekwueme
Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya a Jamhuriyya ta biyu,Dakta Alex Ifeanyichukwu Ekwueme ya rasu a watan Nawumba a wani asibiti dake birnin London. Ya rasu yana da shekaru 85.
Kasimu Yero
Kasimo Yero, Shahararren dan wasan kwaikwayo ne dake yin fina-finan Hausa da na Turanci, ya rasu a Kaduna a watan Satumba. Marigayi Kasimo Yero ya rasu yana mai shekaru 70 bayan yayi doguwar jinya.
Sarkin Katagum, Kabir Umar
Sarkin Katagum Alhaji Kabir Umar ya rasu a watan Disamba bayan yayi jinya a Asibiti. Ya rasu ne a garin Azare jihar Bauchi. Sarkin ya rasu yana da shekaru 89.
Gidado Idris
Gidado Idris, tsohon sekatare gwamnatin Najeriya a lokacin mulkin janar ,Sani Abacha, ya rasu a watan Disamba yana mai shekaru 82.
Ya yi karatu a Najeriya da Ingila, kuma ya rike mukamin Sakatare na Musamman ga marigayi Ahmadu Bello, Sardaunan Sokoto.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng