2018: CAN ta bukaci 'yan Najeriya su goyi bayan Shugaba Buhari
- Kungiyar Kristocin Najeriya CAN ta bukaci yan Najeriya su goyi bayan gwamnatin shugaba Buhari
- Bishof Tunde Akinsanya yayi kira ga yan Najeriya su jajirce wajen yi wa shugaban kasa adu’o’i dan samu nasara a gwamnatin sa
Kungiyar Kristocin Najeriya (CAN), ta bukaci yan Najeriya su cigaba da goyon bayan gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, akan kokarin farfado da tattalin arzikin kasar da ya ke yi.
Shugaban kungiyar CAN reshen jihar Ogun, Bishof Tunde Akinsanya, ya bayyyana haka ne a ranar Litinin a lokacin da yake zantawa da manema labaru a Abeokuta.
Akinsanya ya bukaci yan Najeriya su jajirce wajen yi wa shugaban kasa adu’a saboda ya samu nasarar kamamla duka ayyukan da ya fara.

Malamin yayi kira ga 'yan Najeriya su yi wa Allah godiya da yasa suka kara ganin sabuwar shekara duk da matsalolin da kasar ta fuskanta a shekara 2017.
KU KARANTA : Zan shiga kafar wando daya da masu boye fetur — Buhari
“Ya zama dole ga al’ummar Najeriya su rika yiwa kasar adu’a Allah ya kare ta, kuma mu rika sa Allah a gaban mu ko mai za mu yi.
Adu’a ce kadai za ta iya magance matsalolin da kasar mu ke fuskanta, idan muka hada kai muka yi adu’a tare, duka matsalolin da kasar ke fuskanta za ta zo karshe.
Mallamin addinin yayi kira da gwamati tarayya da kada ta gaza wajen cigaba yaki da cin hanci da rashawa a kasar.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng